Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta daidaita albashin ma’aikatan lafiya na jihar da na takwarorinsu da ke aiki a gwamnatin tarayya, domin inganta jin daɗinsu da rage ƙaurar ƙwararrun ma’aikatan zuwa wasu jihohi da ƙasashen ƙetare.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da gidan rediyon Premier Radio.
Ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na samar da ingantaccen yanayin aiki, ƙarfafa gwiwar ma’aikatan lafiya da kuma tabbatar da cewa sun ci gaba da gudanar da ayyukansu a Kano.
Kwamishinan ya jaddada cewa kyautata walwalar ma’aikatan lafiya da samar musu da yanayin aiki mai kyau na da muhimmanci wajen inganta harkokin kiwon lafiya da tabbatar da ingantaccen kulawa ga al’umma.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da ɗaukar matakan da za su bunƙasa harkar lafiya tare da ƙarfafa gwiwar ƙwararrun ma’aikata su ci gaba da zama a jihar, maimakon ƙaura zuwa wasu wurare domin neman ingantaccen albashi da yanayin aiki.
Wakilinmu, Kamal Umar Kurna, ya rawaito cewa kwamishinan ya bayyana hakan ne a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen gwamnati na inganta harkar lafiya da jin daɗin ma’aikatan jihar.
