Sanatan Kano ta Kudu, Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila, ya ce kare rayuka da dukiyoyi, da samar da ƙudurorin da za su inganta rayuwar al’umma da ciyar da yankin gaba, su ne ginshiƙan ayyukan da ya mayar da hankali a kai cikin shekaru uku da ya shafe a Majalisar Dattawan Najeriya.
Sanatan ya bayyana hakan ne lokacin da yake jagorantar bayar da tallafin kekunan ɗinki 450, da babura 400 da motoci 16 ga shugannin jam’iyyar APC da al’ummar ƙananan hukumomi 16 na Kano ta kudu da yake wakilta.
Kawu, ya ce ya kawo ayyukan da suka tallafawa lamuran tsaro, noma, ilimi, kiwon lafiya da samar da ruwa a yankin, inda ya ce ya gina tare da gyara makarantu, da tallafawa ɗalibai sama da dubu ɗaya wajen karatunsu a jami’o’i da sauran manyan makarantu, ciki har da kwalejojin lafiya duk da ƙalubalen tattalin arziki da ake fuskanta.
A nasa jawabin, Shugaban jam’iyyar APC na Kano Umar Haruna Doguwa yayi alƙawari tare da barazanar sauke duk shugaban jam’iyyar APCn da aka samu da siyar da mota ko babur ɗin da aka bashi daga mukaminsa, inda ya hore su da su yi amfani tallafin wajen ayyukan jam’iyya da haɓaka tattalin arzikin jihar Kano.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Sanata Kawu Sumaila na cewa ya kuma gudanar da aikin gina manyan asibitoci guda biyu, inda aka kammala ɗaya a Zanewa, yayin da ake ci gaba da gina ɗayan a Ƙaramar Hukumar Ajingi.
