
Aminu Abdullahi Ibrahim
Harin martani ne ga hare-haren da Amurka ta kai wasu sassan Iran a daren jiya Talata bayan da ta zargi Iran da harbo jirginta samfarin Helkwabta a tsibirin Hormuz.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce kasar sa zata mayar da martani ga duk wata barazana ko farmaki da Amurka ta kai musu.
Ya ce idan har Amurka tana son zaman lafiya to ta bar nahiyar Asia.
Tuni dai kasashen duniya suka fara nuna fargaba dangane da sabon yakin da ya barke a tsakanin kasashen Amurka da Isra’ila da kuma Iran.
