Gwamnatin Kano ta fara gudanar da gwajin lafiya ga ma’aurata 3,000 da za ta daurawa aure a karkashin shirin auren gata, domin tabbatar da ganin sun shiga rayuwar aure cikin koshin lafiya ba tare da suna ɗauke da cututtuka masu yaɗuwa ba.
Shugaban Hukumar kula da dakile yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki ta Kanjamau da sauran cututtuka masu yaɗuwa ta Kano Dr Usman Bashir ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai lokacin da aka fara gudanar da gwaje-gwajen.
Dr Usman ya ce gwaje-gwajen sun haɗa da na cutar kanjamau (HIV), ciwon hanta, cutar amosanin jini (Sickler) da sauran cututtukan da ake iya ɗauka ta hanyar saduwar aure, da sauran cututtuka masu yaɗuwa, domin tabbatar da lafiyar ma’auratan.
Dr Usman Bashir ya bayyana cewa yin gwajin na daya daga cikin matakan da ake bi cikin ƙoƙarin gwamnati na kare lafiyar al’umma da kuma rage yaɗuwar cuta tsakanin ma’aurata.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Daraktan na yin kira ga ma’auratan da su bada cikakken haɗin kai wajen gudanar da gwaje-gwajen, tare da jaddada cewa sakamakon gwajin zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da walwalar iyali a nan gaba.
