Saurari premier Radio
26.4 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa sunan Ummi Rahab matashiya ta yaudari wani naira 800,000

Da sunan Ummi Rahab matashiya ta yaudari wani naira 800,000

Date:

Rundunar ‘yan sandan Kano takama wata matashiya dake basaja a matsayin jarumar fina finan hausa Ummi Rahab.

Mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama wacce ake zargi Nusaiba Yahaya, ‘yar shekara 18 dake zaune a unguwar Hotoro a Juma’ar nan.

Ya ce wani mutum dan asalin jihar Kano mazaunin kasar Amurka ne ya shigar da kara gaban rundunar yana zargin ta da yaudarar sa a shafin Facebook da sunan Ummi Rahab.

A cewar SP Kiyawa, matashin sunyi soyayya harda alkawarin aure da ita bayan tura mata kudade da yayi kafin daga bisani ya gano ba Ummi Rahab din bace ta gaskiya.

A nata bangaren Nusaiba Yahya, ta tabbatar da cewa hakika ta bude shafin Facebook da sunan ummi Rahab wanda hakan ya bata damar cin kudin matashin.

Tace daga lokacin da suka hadu taci masa kudi kimanin naira dubu dari takwas da waya Iphone 11 pro max.

Sai dai tace matashin da kansa ya bude mata hanyar da zata ci kudin sa ta hanyar tambayar ta abinda takeso.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...