Ministan kiwon lafiya na Jamhuriyar demokkuradiyyar Congo Samuel Kamba ya bayyana cewa cutar da ta bullo a ƙasar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 153 daga cikin mutane 626 da aka gano sun kamu da ita.
Ministan ya bayyana yankunan Ituri dake karkashin ikon jihar Bunia da yankin Mongwalu da lamarin ya fi kamari,duk da cewa akwai wasu yankuna da cutar ta bulla.
Ya zuwa wannan lokaci arewacin Kivu ne cutar ta bayyana inda aka gano mutum daya da ya kamu da ita, biyu a Butembo wacce ba ta tsaya a nan ba, ta kuma bazu zuwa kudancin Kivu.
Rahotanni daga yankunan da ke karkashin ikon ƴan tawayen M23 an samu bullar cutar bayan gano mutun daya da ya kamu da cutar a garin Mitiu.
A Rwampara, kimanin kilomita goma daga Bunia, dangin wani majinyaci da ya mutu sakamakon cutar Ebola sun cinnawa tantunan cibiyar kula da marasa lafiya wuta a ranar Alhamis.
Lamarin dai ya faru ne bayan ma’aikatan lafiya sun ƙi mika gawar ga dangin mutumin da ya mutu.
Hukumomin a ƙasar sun bayyana takaicin su, tare da kira ga al’umma na ganin sun bayar da haɗin kai a wannan yaƙi da cutar ta Ebola.
Yanzu haka ƙungiyoyi da dama ne suka soma isa ƙasar da nufin kai ɗauki yankunan da cutar ta ɓulla.
