Ƙasar China ta fara aiwatar da manufar cire haraji kan kayayyakin da take shigowa da su daga ƙasashen Afirka 53, inda Eswatini kaɗai aka ware daga cikin ƙasashen da za su amfana da shirin.
Matakin, wanda ya fara aiki a ranar 1 ga Mayun 2026, ya faɗaɗa manufar cinikayya marar haraji da China ta fara aiwatarwa tun Disambar 2024, wadda a wancan lokacin ta shafi ƙasashen Afirka 33 masu ƙarancin ci gaban tattalin arziki.
Gwamnatin China ta ce manufar na da nufin ƙarfafa hulɗar tattalin arziki da ƙasashen Afirka, tare da buɗe ƙarin damarmakin kasuwanci da za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin ɓangarorin biyu.
Sai dai an cire ƙasar Eswatini daga cikin shirin saboda alaƙar diflomasiyyarta da Taiwan, wadda China ke ɗauka a matsayin wani ɓangare na ƙasarta.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauye a tsarin cinikayyar duniya, musamman bayan matakan ƙarin harajin shigo da kaya da gwamnatin Amurka ta kakabawa wasu ƙasashe, ciki har da ƙasashen Afirka.
Ana kallon wannan manufar a matsayin wani sabon mataki na faɗaɗa damar kayayyakin Afirka shiga babbar kasuwar China.
