Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBINCIKE:Yadda aka yi sama da fadi da miliyoyi kudin aikin samar da...

BINCIKE:Yadda aka yi sama da fadi da miliyoyi kudin aikin samar da ruwan sha a Kano

Date:

Daga Aisha Ahmad Isma’il

 

Amira karamar yarinya mai shekaru 9 kacal a duniya, sai dai duk kankantar shekarunta an hangota tana tura kurar ruwa mai dauke da jarkoki hudu.

 

Ko da ya ke da muka tuntubi Amira ta daliba ce a makarantar Firamare Kore da ke karamar hukumar Makoda.

 

Amira yar mitsitsiyar yarinya ta ɗebo ruwan ne daga wata ƙorama mai nisan kilimota 10 daga gidan su.

 

A kowace safiya, yarinyar mai shekaru tara kan haÉ—u da sauran Æ´an uwanta yara dake yankin Kore don É—ebo ruwan, kafin daga baya su shirya su tafi makaranta.

 

Mafi yawancin lokuta, yaran kan makara, har ma akan dakatar da su na wani lokaci a matsayin ladabtarwa, duk don tafiya É—ebo ruwan da su suke yi.

 

Kadija Haladu ita ce mahaifiyar Amira ta ce, matslar ruwa na dagula musu lissafi ta yadda yake shafar rayuwarsu ta yau da kullum.

 

Ta ce yaranta bakwai kan rasa karatu na wasu lokuta saboda yawon nemo ruwan sha da na amfanin yau da kullum daga guri mai nisa.

 

Kusan kilomita 20 daga Kore, a ƙaramar hukumar ta Makoɗa, tawagar mu ta hango wani ɗan ga ruwa a Dunawa yana ɗiban ruwan da zai siyar ga kwastomomin sa.

Duk da ruwan bashi da tsafta kuma kamar yana ɗauke da ƙwayoyin cutuka, amma a cewar ɗan ga ruwan, ruwan da zai iya samu ke nan a wannan lokaci.

 

Da yake yi mana ƙarin bayani, Shugaban ƴan ga ruwan yankin, Musbahu Abubakar yace, ya zama ɗan ga ruwa ne saboda dalilai guda biyu; rashin aikin yi da rashin ruwa a yankin.

 

Yace baya karɓar kuɗi da yawa, don Naira shirin kacal ake biya kan kowace jarka.

 

“Kura ta na cin jarkoki 12, kuma ina cinikin kusan N2,400 a kullum don ciyar da iyali na,” in ji shi.

 

Yace tuƙa-tuƙan da suke da shi wanda aka gina shekaru huɗu da suka gabata, yanzu haka baya aiki.

Ruwan rijiyar da al’ummar Dunawa da ke sha da amfanin yau da kullum

Abdullahi Usman Galadima, shi ne Mai Unguwar Dunawa, kuma ma’aikacin lafiya, ya ce yankin sa bai mori tagomashin aikin da ake yiwa mazaÉ“u ba, musamman ta fuskar samar da ruwan sha tun lokacin wakilin su, Umaru Inusa Mai Tsidau tun shekarar 2015.

Mai Umguwar Dunawa Abdulah Usman Galadima

“Idan za mu samu ruwan famfo, za mu ji daɗi sosai. Yanzu haka fa akwai yankunan da basu da ruwa kwata-kwata a karamar hukumar Makoɗa.

 

Dole sai mutanen yankunan sun shigo cikin garin MakoÉ—a don su sayi ruwa ko kuma su nema wajen Æ´an ga ruwa, kuma suna bayar da Naira hamsin saboda nisan da suke da shi da ga cikin garin,” in ji shi.

 

Galadima ya alaÆ™anta wasu cutuka da ake fama da su a yankin da Æ™arancin ruwan. Sai dai ya ce daga lokaci zuwa lokaci, Ma’aikatar Muhalli kan aiki jami’anta su  zuba alumun da wasu sinadarai kamar chlorine, corrosion inhibition, antifoaming da sauran su don tsaftace ruwan.

 

A yankin Koren Tabo a dai karamar hukumar Makoɗan, wani dattijo, Yusuf Ali Gatseka, cewa yayi famfon tuƙa-tuƙa ɗaya gare su, kuma ya shafe shekaru 35 a yankin.

 

A cewar sa wasu lokutan ma sai tuÆ™a-tuÆ™an ya É—auki wata guda baya aiki wanda haka ya sanya al’ummar yankin amfani da ruwan wani tafi wanda ya kai nisan kilomita a tafiya, a dawowa ma kilimota goma.

 

“A kullum a kan yi amfani da ruwa jarka ashirin a gida na a kullum, sai dai nisan gida na da cikin birni na kawo tsaiko wajen gudanar da ayyukan a gidan,” Inji Gatseka.

Yusuf Ali Gatseka, Dattijo Mazaunin Koren Tabo a Makoda 

Rashin ruwa a wannan yanki ma yana da alaƙa da rashin gudanar da aikin samar da fanfo a yankin da gwamnati ta bawa kamfanin Sabon Ruwa General Investments Limited a wata kwangila da aka fitar da Naira Miliyan 3 don aiwatar wa.

 

A binciken da wannan wakiliyar ta gudanar ya nuna cewa kamfanin Sabon Ruwa General Limited, kamfani ne mai zaman kan sa, kuma shafukan nan dake tattara bayanan kamfanoni a ƙasar nan NigeriaCheck, da b2bhint sun nuna a yanzu kamfanin baya aiki wato inactive.

 

A cewar shafin Corporate Affairs Commission (CAC), wato hukumar nan dake yiwa kamfanoni rajista a kasar nan, kamfani na zama mara aiki, wato inactive idan hukumomin gudanarwar sa basu bayar da bayanan abinda suke samu duk shekara ba.

 

Kuma bayar da kwangila ga irin wadannan kamfanoni, kamar na Sabon Ruwa General Investment Limited ya saɓa da sashi 4.4 na dokar Public Procurement Act, 2007.

 

A gefe guda kuma lauyoyi sun bayyana yadda ita hukumar ta CAC kan sha’afa wajen sanya bayanan kamfanonin da suke mika mata bayanan su duk shekara, don haka ne ma ba za’a ga laifin su ba don gazawar hukumar wajen yin aikin ta.

 

An tabbatar da samuwar kamfanin Sabon Ruwa General Investments Limited, ranar 16 July, 2018, tare da lambar rajista 1510565. Duk kokarin da muka yi na samun kamfanin a adireshin sa a lamba 6 Kard Shops, Gandu Albasa quarters, Kano, amma hakan mu bai cimma ruwa ba. Wakilan mu da suka halarci unguwar Gandun Albasa basu sami gani adireshin kamfanin ba, kuma al’ummar dake yankin sun bayyana cewa basu da masaniyar kamfanin a yankin.

Ganin yanayin ruwan rijiyar da Æ´an ga ruwa da sauran al’umma a yankin Kore a ke amfani da shi ya sanya miÆ™a samfurin ruwan ranar 5 ga Nuwambar 2022, ga MAMS Consultancy Services, dake Kano don gwaji.

 

Bayan kwanaki uku sakamakon ya fito tare bayyana cewa ruwan bashi da tsaftar da ya kamata a sha domin yana ɗauke da ƙwayoyin halitta masu cutar da lafiyar ɗan Adam.

 

Sakamakon gwajin ya nuna ruwan na É—auke da wasu Æ™wayoyin halitta nau’in bacteria da ake kira Psedomonas aeruginosa, wanda idan su kayi yawa a cikin ruwa, suna haddasa amai, ciwon ciki da zazzaÉ“i.

Gwajin ya kuma nuna wasu ƙwayoyin halittar dake nuna cewa bahaya ya gurɓata ruwan, da kuma wasu ƙwayoyin masu haddasa cutuka iri iri ciki har da amai atini, ciwon hanta, typhoid da wasun su.

Al’ummar Koren Tabo dake karamar hukumar Makoda kan É—ebo ruwa daga wannan kogi daga lokaci zuwa lokaci

 

Yadda Wasu Ƙananan Hukumomin Ke Fama Da Ƙarancin Ruwa

 

A shekarar 2019 ne wani rahoton Ma’aikatar Ruwa ta kasa da Æ™ungiyar by the Federal Ministry of Water Resources and Asusun Yara da Ilimi na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya nuna cewa É—aya cikin uku na al’ummar Najeriya na shan ruwa mara tsafta, inda yara 130,000 ne ke mutuwa duk shekara sakamakon cutukan da ake samu daga ruwa mara tsafta a Æ™asar.

 

A cewar UNICEF, samun tsaftataccen ruwan sha na ci gaba da zama ƙalubale mai girma ga yan Najeriya musamman mazauna karkara inda kimanin mutane miliyan 69 basu da yadda zasu samu ruwa mai tsafta, sannan mazauna karkara mutum miliyan 19 ke shan doguwar tafiya kafin su samu ruwan sha da amfani, daga ƙoramu, rafuka da koguna.

 

Don magance wannan matsalar ne ma gwamnatin tarayya, ta cikin ayyukan da Æ´an majalisu ke kaiwa al’ummar su wato constituency projects, ma’aikatar ayyuka, gidaje da sufuri ta bawa kamfanin Azaico Construction Nig Naira miliyan, 180, 000 don gina famfo 30 masu inci a mazaÉ“ar Fassi dake Æ™aramar hukumar Kibiya.

 

Sai dai binciken mu na gano cewa ba’a gudanar da wannan aiki ba.

 

A cewar Mai Unguwar Fassi, Ado Sa’adu su dai basu ha wani aikin samar da famfon ko tuƙa-tuƙa a yankin ba.

 

“Mu kan haka rijiyoyi. Wasu wuraren ruwan da daÉ—i wasu kuma da zartsi, amma yawanci ana samun ruwa mai daÉ—i saboda muna da yashi sosai, ruwan yana da kyau kuma yana shayuwa.”

 

Yace sai dai za su ji daɗi sosai idan aka samar musu da fanfon tuƙa-tuƙa, domin kuwa zai saukakawa mazauna yankin ayyukan su na yau da kullum.

 

A yankin Kwantagi dake mazaɓar in Fassi ward ma batun kusan guda ne. Isa Muhammad Dauda, wani mazaunin yankin ne, kuma ya shaida mana cewa tuƙa-tuƙan da suke da shi a yankin wanda ya shafe kusan shekaru shida da ginawa ya lalace.

 

Wani mazaunin yankin, yace rabon su da ganin gwamnati ta gina sabon burtsatse shekaru shida ke nan, amma a cewar sa suna samun tallafi daga kungiyoyi masu zaman kan su daga lokaci zuwa lokaci.

Dauda, wanda ke sana’ar Siyar da shayi yace rashin ruwan a kusa na kawo cikas ga sana’ar sa, domin burtsatsen da ake da su sun lalace, duk kuwa da kokarin al’ummar yankin na gyarawa.

Wani burtsatse a Kwatangi, Fassi dake ƙaramar hukumar Kibiya

 

A binciken da muka gudanar kan kamfanin Azaico Construction Nig a shafin NigeriaCheck, ya nuna cewa an yiwa kamfanin rajista da adireshin sa a lamba 10, Gaida Panshekara dake karamar hukumar Kumbotso a Kano. Amma duk kokarin da muka yi na gano kamfanin ya ci tura. Ko a ziyarar da muka ka adireshin a ranar 7 ga Nuwambar 2022, bamu ga kamfanin ba.

 

Kuma mazauna yankin sun ce basu san da kamfani mai irin sunan a yankin ba. Haka ma tura saƙo ta adireshin email ɗin da kamfanin yayi rajista da shi na azaicoconstructionnigltd@gmail.com, amma saƙon yaƙi tafiya,tare da ƙarin bayanin babu wanda ke amfani da adireshin.

 

 

A ƙaramar hukumar Bunkure kuwa, an baya kamfanin Halliru Gurjiya and Sons Ltd kwangilar samar da famfo 110 kan kuɗi N8,464,500 da burtsatse guda 112 kan kuɗi N1,814,400.00.

 

Wasu yara kenan yayin da suke É—inan ruwa a yankin Bono dake karamar hukumar Bunkure

 

Wani mazaunin Bono dake karamar hukumar Bunkure, Sabo MaiKifi Auwal ya ce dukkan rijiyoyin burtsatsen da suke da su babu wanda gwamnati ta gina musu, sai dai wasu bayin Allah ne ke taimaka musu.

 

Auwal, wanda ke sana’ar siyar da kifi yace rashin samun ruwan na kawo wa sana’ar shi cikas, domin baya samun wanke kifin sa yadda ya kamata.

Wani Mazaunin Bono da ke karamar hukumar Bunkure  Sabo Mai Kifi Auwal,

 

Shin ma kamfanin da muka gano yayi rajista a adireshi mai lamba 1, No.1 Taura road, opposite NNPC Hotoro, Kano, babu alamar da a wannan waje.

 

Wani mazaunin yankin Muhammad Haruna yace ya dade a wannan waje kuma bai san da zaman kamfanin ba.

 

Bayan ziyartar wurare da dama a karamar hukumar Bunkure, (Bono, Agalawa, da Sabon gari) don tattaunawa da mazauna yankin, Shugaban jam’iyyar a karamar hukumar, Rabi’u Halliru basu ga an gina ko kawo fanfo yankin ba. Yace duk wani aikin samar da ruwa a yankin wanda gwamnatin jihar ta aiwatar ne ba na tarayya ba.

Ana Amfani Da Ayyukan MazaÉ“u Wajen Almundahanar KuÉ—in Jama’a – Masani

 

A zantawar sa da wakiliyar mu, wani Jami’i a kungiyar wayar da kan al’umma da tabbatar da adalci ta CAJA, Akibu Hamisu yace sai da yawa wakilan jama’a na amfani da ayyukan da suke kawowa mazaban su wajen tatsar kuÉ—in talakawa.

 

Yace a matsayin su na É—aya daga masu sanya idanu kan irin wadannan ayyuka, sun gano yadda ake aiwatar da ayyuka marasa inganci, a wasu wuraren ma ba za’a gudanar da su ba.

 

Jami’ai yace sun kuma gano yadda hakan ke faruwa domin mafi yawanci Æ´an majalisun kan bawa kamfanonin su aikin ko kamfanin wani na kusa da su.

 

” Wadannan ayyuka ne da ake samun kuÉ—i da su sosai, sai dai hukumomin yaÆ™i da cin hanci, da kungiyoyin al’umma da ma Æ´an jarida na kokari matuka wajen ganin an samu raguwar irin wadannan halaye,” In ji shi.

 

Ya bayyana bukatar dake akwai na ganin ana bawa kowane kamfani damar neman irin wadannan kwangiloli don samun ayyuka masu inganci.

 

Ana Zargin ÆŠan Kwangila Da Aiki Mara Inganci A Falgore

 

A shekarar 2019 ne dan majalisa mai wakiltar Doguwa/Tudun Wada, Alhassan Ado Doguwa ya mikawa majalisar bukatar al’ummar sa na samar da famfon burtsatsen masu amfani da hasken rana.

 

A kasafin wannan shekara ne aka fitar da kudi Naira miliyan É—ari tare da bawa kamfanin SAT Engine Services don gina famfon burtsatsen guda goma.

 

A ziyarar ganibda ido da muka kai, mun gano cewa da yawa daga fanfon burtsatsen a yankunan Brunburun, Bul, Falgore, Rugurugu, da Janduste basa aiki, kamar yadda jama’ar garin suke zargin É—an kwangilar da aiki mara inganci.

 

Wani shuguba a hannun Rugurugu, Sani Umar yace fanfon burtsatsen ya daina aiki watanni hudu bayan kammala shi, kuma har yan sun kasa gyara shi saboda basu da kuÉ—n yin hakan.

 

Haka wani aikin famfon a yankin Falgore dake Doguwa baya aiki, inda jama’ar yankin suka shaida mana cewa watanni shida kacal da kammala shi ya daina aiki.

 

Mutanen yankin sun ce an miƙa musu ayyukan ne a watannin Fabrairun 2021 da Agustan 2021.

 

Abdullahi Aliyu, wani shugaba ne a yankin, ya kuma shaida ma a cewar dattijawan yankin daga bisani sun yanke shawarar a É—auke sauran kayan aikin a É“oye su don gudun kada É“ata gari su sace.

 

“Famfon burtsatsen ya nutse ne don Æ™asar wurin na da laushi sosai. Ko a farkon aikin mun bawa É—an kwangilar shawarar kada a gina a wajen, amma suka share mu. Watanni shida bayan kammala shi kuwa aikin ya rufta,” in ji shi.

 

Ya ƙara da cewa sun yi kokarin sake neman ɗan kwangilar, da wakilin su don mika koken su, amma abin ya ci tura.

 

A ƙarin hasken da yayi mana, Kabiru Ado, wani kwararre a harkar duba ingancin ƙasa da kamfanin Munib Drilling Company dake Fagge a Kano yace akan samu irin wannan matsala ne idan ƴan kwangilar basu gudanar da bincike kan ƙasar inda zasu yi aiki yadda ya kamata ba.

 

Ya kuma ce wasu lokutan masu haka rijiyoyin basa kai zurfin da ya kamata, wanda hakan na taka rawa wajen rashin ruwa yadda ake so.

 

Na tuntuÉ“i hukumar Hadejia Jamaare, wanda ta hannun ta aka bayar da wannan kwangila, inda hukumar ta bayyana cewa al’ummar yankin ke da alhakin gyara duk wani fanfon burtsatsen da ya samu matsala a yankin su.

 

Mustapha Umar, shi ne shugaban sashen samar da ruwan sha a hukumar, ya kuma bayyana mun cewar mafi yawan lokuta al’ummar yankunan da aka yiwa irin wadannan ayyuka basa mayar da hankali wajen gyara matsalolin da kan taso.

 

” Wasu lokutan gyaran bai taka kara ya karya ba, amma saboda basu É—auke su a matsayin ayyukan a matsayin na Æ™ashin kan su ba, sai su Æ™i gyarawa. Yanzu haka kuma kokarin wayar da kai da da bayar da horo ga al’ummar irin wadannan ayyuka kan yadda za su dinga gyara matsalolin da kan iya faruwa ga fanfunan burtsatsen su,” inji shi.

 

Umar ya kuma yi alkawarin gyaran dukkan fanfanun da suka samu matsala a mazaɓar ta Doguwa/Tudunwada nan ba da jimawa ba.

 

Ko na na nemi zantawa da shugaban hukumar tHadejia-Jama’are, kakakin ta ya bayyana cewa hakan zai dauki lokaci mai tsawo ganin shugaban dake jagorantar hukumar a yanzu ba shi ne a lokacin da aka gudanar da ayyukan ba.

 

“Ina fatan amsar da muka baki za ta isa a yanzu, domin dole sai an nemo wadanda suka yi aikin a wancan lokaci wato shekaru shida baya, a zauna na tsawon lokaci domin su yiwa Darkatan bayanan da suka dace,” he added.

 

Da wakiliyar ta mu ta tuntuɓi Daraktan a kamfanin SAT Engines Service, Alhaji Saminu Adamu, yace su dai a bangaren su sun gudanar da aikin yadda ya kamata.

 

Ya ce “ko da bayan mun kammala aiki ne da watanni ukun da ake iya dawo damu idan da matsala, muna komawa mu taimakawa al’ummar inda muka yi aiki gyara matsalar da suka samu.”

 

Yace lokacin da suka mikawa al’ummar yankin, dukkan fanfon tuka tukan na aiki yadda ya kamata.

 

Ya Æ™ara da cewa “Karamar hukumar ko al’ummar yankunan da aka yi wadannan ayyuka ba za su iya kula da su yadda ya kamata ba. Ni zan bayar da shawarar gwamnati ta dinga miÆ™a irin wadannan ayyuka ga Æ´an kasuwa, su kuma su nemi al’ummar yankunan su dinga biyan wani abu na ruwan da za su É—iba”.

Ma’aikatar Da abin ya shafa bata bamu amsa ba

 

Mun aikewa da ma’aikatar ayyuka, gidaje da sufuri da takaddar neman bayanai wato FOI a ranar ga watan Nuwamban 2022, har zuwa wallafa wannan bincike basu ce komai kan batun ba.

Aniyah Media Consulting Limited

 

“Wannan rahoto cibiyar binciken kwakwafi ta ICIR da gidauniyar John D. T. MacArthur suka dauki nauyin gudanar da shi”

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...