
Aminu Abdullahi Ibrahim
Majalisar dokokin jihar Kano ta kafa kwamiti mai mutane 12, domin tantance Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan Kano.
Kakakin majalisar Jibril Ismail Falgore ne ya sanar da kafa kwamitin tare da bukatar gabatar da rahotonsa kafin ranar Litinin don tantance Garo
Wakiliyarmu ta majalisa dokokin Kano Binta Khalid Muhammad ta ruwaito cewa an kafa kwamitin ne bayan da kakakin majalisar a zaman yau Laraba ya sanar da karba wasikar da gwamnan Kano ya aike don neman amincewar majalisar domin ya nada Garo a matsayin mataimakinsa.
Tuni aka nada mataimakin shugaban majalisar Muhammad Bello Butu-Butu a matsayin shugaban kwamitin tantance sabon mataimakin gwamnan, domin tattara bayanansa tare da mikawa majalisar don daukar mataki na gaba.
