Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiBello Turji ya ƙaryata iƙirarin da sojojin Nijar suka yi na kama...

Bello Turji ya ƙaryata iƙirarin da sojojin Nijar suka yi na kama mashahurin ɗan bindigar nan Baleri.

Date:

Gawurtaccen ɗan bindigar nan na da gwamanti ke nema ruwa ijallo  Bello Turji ya ƙaryata iƙirarin da sojojin Nijar suka yi na kama mashahurin ɗan bindigar nan Baleri.

Wannan na zuwa ne ta cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, in da aka ga Bello Turji, kewaye da mayaƙansa riƙe da muggan makamai, ya na nuna wani mutum da ya ce shi ne Balerin, ba wanda sojojin Nijar suka ce sun kama ba.

A dai makon da ya gabata ne Jaridar PRNigeria ta yi wani bincike da ya  tabbatar da cewa mutumin da sojojin Nijar suka kama sunansa Kachalla Baleri, ba Baleri Fakai da sojojin Najeriya ke nema ruwa a jallo ba.

Cikin bidiyon mai tsawon minti ɗaya da sakan 29, Bello Turji ya zargi gwamnatocin Nijar da Najeriya da kamawa tare da kashe mutanen da ba su ji, ba su gani ba a matsayin ‘yan bindiga.

Sojojin kasar nan dai sun bayyana samun gagarumar nasara dangane da kamen da sojojin na Nijar ɗin suka yi, to sai dai binciken PRNigeria da wannan sabon bidiyon ka iya aza ayar tambaya kan sahihancin iƙirarin nasu.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...