Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBayan Tinubu, Kwankwaso Zai Yi Jawabi A Chatham House.

Bayan Tinubu, Kwankwaso Zai Yi Jawabi A Chatham House.

Date:

A gobe Laraba dan takarar shugaban kasa na jami’iyyar NNPP, Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso zai gabatar da jawabi a cibiyar bincike kan manufofi da kuma kudure-kuduren gwamnatocin ƙasashe a duniya ta Chatham House da ke Ingila.

 

Kwankwaso dai zai gabatar da jawabin ne kan manufofinsa na son zama shugaba Najeriya, da karfe biyu na rana.

 

Chatham house dai ta kasance cibiya mai zaman kanta da ba ta gwamnati ba, wadda ta fi mayar da hankali kan abubuwa da dama na lafiya da ci gaba da tattalin arziki da hada-hadar ƙasa da ƙasa da sauransu.

 

Cibiyar na kuma da muhimmancin gaske saboda ƙasashen duniya da dama sun yarda da inganci da sahihancin bincike da suke gudanarwa kan shugabanci da manufofi ko kudurorin gwamnati.

 

A kwanakin baya dai dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar da jawabi a cibiyar.

 

Ana kuma sa ran shima dan takarar shugaban kasa na jam’iyyun Peter Obi zai kai ziyara cibiyar.

Latest stories

Related stories