Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS, tace an samu saukar farashin kayayyaki a sassan kasar a cikin watan Disambar bara.
Alkaluman da hukumar ya nuna cewa tsadar rayuwar ta ragu zuwa kashi 21.34 daga kashi 21.47 da aka gani a watan Nuwamba 2022, yayin da tsadar kayayyakin masarufi ya sauka daga kasha 24.13 zuwa kashi 23.75.
Wannan na zuwa ne duk da cewa akwai matsalar rashin tsayuwar farashi a wasu yankuna na kasar nan.
Saukar farashin a cewar NBS, ya zo ne cikin watan na Disamba dai-dai lokacin da jama’a ke shirin fara bukukuwan Kirsimati da na sabuwar shekara.
Rahoton na NBS ya ce kayayyakin da farashinsu ya sauka sun kunshi na abinci da nau’ikan ababen sha sai kuma farashin sufuri da shi ma ya sauka lamarin da ya samar da sassauci ga tsadar rayuwar da jama’a ke fama da shi.