Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBafarawa, Ya Dora Alhakin Dukkan Matsalolin Da Najeriya Ke Ciki Kan Tsohon...

Bafarawa, Ya Dora Alhakin Dukkan Matsalolin Da Najeriya Ke Ciki Kan Tsohon Shugaban Kasa Buhari

Date:

Tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa, ya dora alhakin dukkan matsalin kasar nan ke fuskanta a yanzu kan tsohon shugaban kasa Muhamadu Buhari.

A wata tattaunawa da jaridar Punch, Bafarawa ya ce babu wanda ya jefa rayuwar yan Najeriya cikin matsala saboda rashin iya shigabanci na Buhari.

Ya Kara da cewa daga Shekara ta 2015 zuwa karshen mulkin tsohon shugaban kasar ya sakwarkwata tsarin da kasar nan ke kai, yana mai cewa maimakon a samu ci gaba sai aka samu koma baya.

Ya bayar da misalai da suka hada da Tsadar Rayuwa da kuma Cin hanci da rashawa saboda rashin iya Jagoranci na tsohon Shugaban Kasar Muhammad Buhari.

Attahiru bafarawa ya bukaci Shugaban kasa bola Ahmad tunubu da ya binciki tsohon Shugaban Kasar saboda yadda aka samu badakala daga jami’an gwamnatinsa.

A baya bayan nan wani rahoton bincike na musamman da Shugaban kasa bola Ahmad tunubu ya bayar da umarni, ya nuna yadda tsohon gwamnan babban bankin kasa CBN, Goodwin Emifele da wasu ministoci har ma da makusantan tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari da wuwure biliyoyin kudade.

Latest stories

Related stories