Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya ce ba zai mayar da mataimakinsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan kallo a gwamnatinsa ba domin magance matsalolin Najeriya idan suka lashe zaɓen 2027.
Obi ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da magoya baya da masu ruwa da tsaki a Enugu, inda ya yi alƙawarin yin aiki kafaɗa da kafaɗa da Kwankwaso wajen magance matsalolin da Najeriya ke fuskanta.
Ya ce gwamnatinsu za ta ba da fifiko wajen tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da ayyana dokar ta-ɓaci a fannin ilimi domin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Obi ya kuma zargi gwamnatin yanzu da gazawa wajen tabbatar da tsaron ’yan Najeriya, yana mai kira ga masu zaɓe da kada su bari farfagandar siyasa ta rinjayi shawararsu.
A nasa ɓangaren, Kwankwaso ya buƙaci ’yan Najeriya su ajiye bambance-bambancen ƙabilanci, su haɗa kai domin magance matsalolin talauci, yunwa, rashin tsaro da rashin aikin yi.
Ya kuma kara da cewe bukaci al’umma su fito kwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri’a, tare da kare kuri’unsu har zuwa lokacin sanar da sakamakon zabe.
Shi kuwa Sanata Victor Umeh ya bayyana tikitin Obi da Kwankwaso a matsayin wanda ya fi dacewa da jagorantar Najeriya a zaɓen 2027.
