
Aminu Abdullahi Ibrahim
Wata ƙungiyar ƙasa da ƙasa mai suna FIAP, tare da haɗin gwiwar FactCheckAfrica, ta kammala horar da ‘yan jarida da masu aikin yaɗa labarai 25 a Kano, kan hanyoyin tabbatar da sahihancin bayanan zaɓe da kuma yaƙi da yaɗa labaran ƙarya a harsunan gida gabanin babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027.
An gudanar da horon na tsawon kwanaki uku, daga ranar 27 zuwa 29 ga Oktoba, 2026, a otal ɗin Comfort Hub Hotels and Suites da ke Kano, inda aka tattauna batutuwan yaɗa bayanan ƙarya, fassarar kalmomin zaɓe, tantance sahihancin labarai da kuma ɗa’a a aikin jarida.

Shirin ya tattaro ‘yan jarida, masu gabatar da shirye-shiryen rediyo, editoci da masu binciken sahihancin bayanai, domin ƙarfafa ƙwarewarsu wajen isar da sahihan bayanan zaɓe ga jama’a cikin harsunan da suke fahimta.
Horarwar ta mayar da hankali kan yadda bayanan zaɓe ke yaɗuwa ta gidajen rediyo, kafafen sada zumunta, saƙonnin murya na WhatsApp da kuma hanyoyin sadarwar al’umma, tare da bayyana yadda kuskuren fassara ko yaɗa bayanan da ba a tantance ba zai iya sauya ma’anar saƙo da kuma ruɗar da masu zaɓe.

An kuma tattauna dabarun yaɗa labaran ƙarya da suka haɗa da ƙirƙirar sanarwar zaɓe, bayar da ranakun zaɓe na ƙarya, umarnin kaɗa ƙuri’a marasa inganci, sauya sakamakon zaɓe da kuma amfani da muryoyin da aka sarrafa domin yaudarar jama’a.
A yayin horon, mahalarta sun yi nazari kan muhimman kalmomin tsarin zaɓe, ciki har da rajistar masu zaɓe, tantance masu zaɓe, rumfunan zaɓe, takardun ƙuri’a, na’urar BVAS, tattara sakamakon zaɓe, laifukan zaɓe da kuma ƙarar zaɓe.

Ɗaya daga cikin muhimman sakamakon horon shi ne duba da kuma inganta daftarin ƙamus na kalmomin zaɓe a harshen Hausa, tare da samar da ƙamus na aiki ga wasu harsunan Arewa da aka wakilta a wajen taron.
Mahalarta sun kuma samar da jagororin amfani da harshe domin taimaka wa ‘yan jarida wajen daidaita rubutun kalmomi, salon magana, taken shugabanni, bambancin harshen hukuma da na yau da kullum, da kuma yadda za a haɗa Hausa da Turanci ba tare da sauya ma’anar bayanai ba.

Da yake magana kan muhimmancin shirin, wanda ya kafa FactCheckAfrica, Abideen Olasupo, ya ce bayanan zaɓe za su amfani jama’a ne kawai idan an isar da su cikin harshen da suke fahimta, tare da kiyaye sahihancinsu da ma’anarsu.
Ya bayyana cewa fassara bayanan zaɓe ba wai sauya kalmomi daga wani harshe zuwa wani ba ne kawai, illa kiyaye ma’anar saƙo da yanayin da aka bayyana shi, domin ‘yan ƙasa su samu bayanan da za su taimaka musu wajen yanke shawara.

Horarwar ta kuma jaddada muhimmancin kula da yadda ake yaɗa labaran da suka shafi mata masu shiga siyasa, masu buƙata ta musamman, ‘yan gudun hijira, da ƙananan kabilu da addinai, domin kauce wa rahotannin da za su iya ƙarfafa wariya ko haifar da rikici.
An kuma koya wa mahalarta dabarun tantance sahihancin bayanai, ciki har da gano asalin majiya, neman tabbaci daga hukumomin da abin ya shafa, kwatanta bayanai daga majiya fiye da ɗaya, da kuma amfani da jerin matakai guda bakwai wajen tantance ingancin labari kafin wallafawa ko karantawa a rediyo.
Shirin ya gudana ne a ƙarƙashin aikin Tarayyar Turai da ke tallafa wa ƙungiyar ƙasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, kan zaman lafiya, tsaro da shugabanci nagari, wanda aka fi sani da EPSG Project.

Taron na Kano shi ne ɓangare na biyu na shirin horarwar da aka gudanar a jihohi biyu, bayan kammala irin wannan horo a jihar Akwa Ibom daga ranar 13 zuwa 15 ga Oktoba, 2026.
A jimlace, shirin ya horar da ma’aikatan kafafen yaɗa labarai 50 daga sassan Najeriya, kan amfani da harsunan gida wajen isar da sahihan bayanan zaɓe, da suka haɗa da Yarbanci, Igbo, Ibibio, Hausa da wasu harsunan Arewa.

Masu shirya taron sun ce za su ci gaba da bibiyar yadda mahalarta ke amfani da ilimin da suka samu da kuma yadda kafafen yaɗa labarai za su haɗa ƙamus da jagororin da aka samar cikin ayyukansu na yau da kullum.
