Gwamnatin Kano ta buƙaci ‘yan siyasa da masu neman muƙamai daban-daban a kowace jam’iyya, da su gudanar da yaƙin neman zaɓensu cikin lumana, mutunta juna da bin ƙa’idojin doka, domin kaucewa duk abinda da zai haifar da rikici a faɗin jihar.
Mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar, biyo bayan damar da Hukumar INEC, ta bayar na fara yaƙin neman zaɓen Gwamna da sauran muƙamai na matakin jiha.
A cewar Bature ya zama wajibi ‘yan takara su mayar da hankali wajen bayyanawa al’umma manufofinsu da tsare-tsaren da suke da niyyar aiwatarwa idan aka zaɓe su, maimakon amfani da kalaman batanci, cin mutunci ko cin zarafin abokan hamayya.
Sunusi Bature ya jaddada cewa fara yaƙin neman zaɓe ba zai kautar DA hankalin gwamnati daga ayyukan raya ƙasa da shirye-shiryen da suka shafi rayuwar al’ummar Kano kai tsaye ba, tare da cewa kowane ɗan takara na da damar bayyana manufofinsa, sannan ya bar al’umma su tantance wanda suka ga ya fi dacewa ya jagorance su.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Sunusi Bature na bayyana cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tabbatar da harkokin siyasa sun gudana bisa tsarin dimokuraɗiyya, zaman lafiya da mutunta juna, tare da bai wa kowa damar gudanar da harkokinsa cikin ’yanci da bin doka.
