
Aminu Abdullahi Ibrahim
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa mutane biyar da gungun ‘yan daban siyasa dauke da makamai suka yi a Kano a ranar Talata 5 ga Mayu 2026.
Amnesty ta ce wannan ya nuna karuwar girman ayyukan ‘yan daba a ‘yan shekarun nan.
Yan daban siyasa sun kashe wani matashi a harabar asibitin KMC da ke Kano
A cewar sanarwa da ta fitar a Larabar nan dole ne hukumomin Najeriya su binciki lamarin domin tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda ake zargi da aikata laifukan da kuma ‘yan siyasar da ke daukar nauyinsu a gaban kuliya.
Sanarwar ta ce wani bidiyo da Amnesty International ta samu ya nuna yadda ‘yan daban ‘yan siyasa masu dauke da makamai ke bin mutanen da suka gudu, wadanda daga baya aka kashe su ta hanyar sara da suka.
Haka zalika a wasu bidiyon, an nuna wadanda aka kashe a cikin jini.
Amnesty ta ce ‘Yan daban dauke da makamai suna sanye da rigar jam’iyya mai mulki suna rera wakoki na barazanar mutuwa.
Ta ce ta samu rahotan yadda magoya bayan wasu ‘yan siyasa ke kai hari ga abokan hamayyar siyasar su.
Amnesty International na binciken sunayen wasu fitattun ‘yan siyasa da jami’an gwamnati a Kano da ake zargin su ne ke daukar nauyin ‘yan daba.
Sanarwar ta ce dole ne hukumomin Najeriya, ‘yan siyasa da jam’iyyun siyasa su girmama doka da oda kuma su tabbatar da cewa suna kare rayuka da dukiyoyi al’umma a lokacin taron siyasa da bayan kammalawa.
