Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaCutar Kwalara ta kashe ƙarin mutum 21 a Jihar Legas.

Cutar Kwalara ta kashe ƙarin mutum 21 a Jihar Legas.

Date:

Cutar Kwalara da ake fama da annobarta ta kashe ƙarin wasu mutum 21 a Jihar Legas kamar yadda mahukunta suka tabbatar.

Bayanai sun ce adadin waɗanda suka kamu da kwalara a fadin jihar ya ƙaru zuwa mutum 401, inda cutar tafi ƙamari a yankunan Lagos Island da Kosofe da kuma Eti-Osa.

Mai bai wa gwamnan shawara ta musamman kan harkokin kiwon lafiya, Dokta Kemi Ogunyemi ce ta tabbatar da hakan.

Ta bayyana cewar adadin waɗanda suka mutu sakamakon barkewar cutar kwalara ya ƙaru zuwa mutum 21, bayan rahotannin da aka samu a baya da ke cewa mutum 350 ne suka kamu kuma 15 ne suka mutu.

Dokta Ogunyemi ta bayyana hakan lokacin da take ƙarin haske game da annobar, bayan da ta gana da mambobin cibiyar ba da agajin gaggawa a fannin kiwon lafiyar al’ummar Jihar Legas.

Ta ƙara da cewar adadin waɗanda cutar ta hallaka ya ƙaru zuwa mutum 21, karin mutane 6 a kan adadin da aka ba da rahoto a baya.

A cewarta, an yi hasashen samun ƙaruwar adadin sakamakon bukukuwan Sallar layya da aka yi, lamarin da ke janyo cunkoson jama’a a wuri guda.

Sai dai ta ce, ana samun raguwar waɗanda ke kamuwa da cutar a ilahirin kananan hukumomin jihar, musamman ma waɗanda a da aka samu ɓullarta saboda ɗaukar matakai da sanya idanu daga gwamnatin jihar.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...