
Aminu Abdullahi Ibrahim
An ƙaddamar da wani sabon shiri na shekaru uku da nufin taimaka wa ’yan mata da suka bar makaranta ko kuma ke cikin haɗarin barin makaranta su koma karatu.
Ƙungiyar DO Take Action, tare da haɗin gwiwar Malala Fund, ce ta ƙaddamar da shirin mai suna REED – Reclaiming Education, wanda zai taimaka wajen aiwatar da manufar gwamnatin Kano ta mayar da ’yan mata makaranta.
A matakin farko, shirin zai gudana a ƙananan hukumomin Madobi, Gezawa da Warawa, inda zai shafi makarantun gwamnati guda 30 da kuma cibiyoyin Islamiyya na al’umma guda 20.

Da take jawabi babbar daraktan kungiyar Do To Action, Precious Ebere Chinonso ta ce babban abin da suke son cimmawa shi ne gano ’yan matan da suka daina zuwa makaranta ko su ke cikin haɗarin dainawa, bibiyar halin da suke ciki da kuma haɗa su da taimakon da zai ba su damar komawa makaranta da ci gaba da karatu.
Ta kara da cewa shirin zai yi amfani da wani tsarin fasaha mai suna Transition Early Warning System, TEWS, wanda aka haɗa da tsarin EDUDATA.
Gwamnatin Tarayya Ta Raba Naira Biliyan 330 A Matsayin Tallafi – Minista Edun
Precious Ebere Chinonso ta kuma ce tsarin zai ba makarantu da cibiyoyin al’umma damar gano ’yan matan da ke cikin haɗarin daina karatu, tare da bibiyar tafiyar karatunsu daga JSS har zuwa SSS 3.
A cikin shekaru biyu na farko, shirin na da burin gano da bibiyar sama da ’yan mata 600 da ke cikin haɗarin barin makaranta, tare da horas da shugabannin makarantu da malamai 100.
Masu shirin sun ce suna fatan a samu akalla kashi 75 cikin 100 na ’yan matan da aka tallafa wa su ci gaba da karatu daga JSS zuwa SSS.
Haka kuma, shirin zai yi aiki da gwamnati domin ganin an samar da kasafin kuɗi na musamman na tallafa wa ’yan mata masu son komawa makaranta, da kuma sanya tsarin TEWS cikin tsarin tsare-tsaren gwamnati na ilimi.
Bayan shekaru biyu na aiwatar da shirin a Kano, ana shirin amfani da abubuwan da aka koya wajen faɗaɗa tsarin zuwa ƙaramar hukumar Madagali a jihar Adamawa a shekara ta uku.
Masu shirin sun ce manufar REED ba wai kawai mayar da ’yan mata makaranta ba ce, illa dai tabbatar da cewa sun ci gaba da karatu har zuwa matakan da za su ba su damar samun cikakkiyar damar ilimi na tsawon shekaru 12.
A nasa bangaren babban sakataren ma’aikatar ilimi na jihar Kano, Bashir Bappa Muhammad, ya ce taron ya mayar da hankali wajen tabbatar da dokar da akayi ta ganin cewa mata suna samun cikakken ilimin da ya dace.
Ya ce a yanzu kididdiga ta nuna cewa yara mata sun fi maza zuwa makaranta a jihar Kano.
Bashir Bappa Muhammad, ya ce gwamnatin Kano ta bayar da motoci wadanda suke bi lungu-lungu suna daukar dalibai mata zuwa makaranta.
Itama daya daga cikin masu fafutukar ganin ‘ya’ya mata sun samu ilimin da ya dace, Ladidi Sani Fagge, ta ce har yanzu akwai karancin kudi da ake fitarwa na tabbatar da cewa dalibai mata na zuwa makaranta da samun kulawar data dace.
Ta kara da cewa akwai bukatar kara gina makarantun mata musamman a yankunan karkara kasancewa da yawa sukan dena zuwa makaranta saboda nisa.
