Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaAl’ummar kasar nan na bayyana damuwa game da yadda gwamnatin tarayya ke...

Al’ummar kasar nan na bayyana damuwa game da yadda gwamnatin tarayya ke ciyo bashin da ya kai tirilyan ashirin cikin shekara guda kacal.

Date:

Al’ummar kasar nan na bayyana damuwa game da yadda gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmad Tinubu ta ciwo bashin da ya kai naira fiye da tirilyan ashirin cikin shekara guda kacal.

Bayanai sun ce wadannan kudi sun fito ne daga basukan da gwamnatin ta karba a cikin gida ta hanyoyi daban- daban da suka hada da takardun lamunin banki, kamar yadda ofishin kula da basuka na kasa.

Binciken da aka gudanar ya nuna cewa tsakanin watan Mayun bara zuwa na bana, gwamnatin ta karbi wannan rance na naira tirilyan 20 da milyan dubu 900 ta hanyar gwanjon takardun kudin bankin da babban bankin kasa ke yi.

Wannan rance bai hada da wadanda gwamnatin ke karbowa daga hukumomin kasashen ketare ba, da suka hada da na bankin duniya da na hukumar bada lamuni ta kiasa-da-kasa ba.

Masana tattalin arziki na bayyana damuwa dangane da irin wadannan matakai da gwamnati ke dauka na karbar rancen cikin gida da suka ce na iya illa ga bangaren ‘yan kasuwa wajen gudanar da harkokin kasuwancinsu.

Nijeriya na fuskantar matsalar karancin kudin gudanar da ayyukan raya kasa, musamman wadanda suka shafi hanyoyi, da samar da ruwansha, da kula da lafiyar jama’a

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...