
Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar zabe ta kasa reshen Kano, ta fara gudanar da aikin rijistar katin zabe a Laraba nan.
A ziyarar gani da ido, da Premier Radio ta je ta ganewa idon ta yadda ma’aikatan INEC ke gudanar da sabuwar rijistar.

An fitar da tsare-tsare ciki har da ware guraren masu bukata ta musamman.
https://premierradio.ng/rkc8
Mai magana da yawun hukumar INEC a nan Kano, Nahila Bello Dandago, ta ce tun safiyar wannan rana ta Laraba, jami’ansu suka isa wurin, domin fara gudanar da aikin katin, tare da kira ga duk wanda shekarunsa ya kai 18, daya garzaya domin samun nashi katin zaben.
https://premierradio.ng/xho7
Hukumar ta INEC, tace rijistar katin zaben na daga cikin shirye-shiryen da hukumar ke yi domin bai wa ‘yan kasa damar mallakar katin zabe kafin babban zaben 2027.
