Kungiyar Masu Shirya Bukukuwa da Masu Wuraren Taro ta Jihar Kano ta sanar da mambobinta cewa jami’an tsaro sun haramta gudanar da duk wani taron siyasa a wuraren shirya bukukuwa da taruka (Event Centres) ba tare da samun izini daga jami’an tsaro ba.
A cikin sanarwar da shugaban kungiyar, Kamalu Mas’ud El-Jibril Doguwa, ya sanya wa hannu, kungiyar ta ce umarnin ya fara aiki ne daga ranar 10 ga Oktoba, 2026.
Sanarwar ta shawarci masu mallakar wuraren taro da su tabbatar duk wanda ke son gudanar da taron siyasa a wurarensu ya fara neman izinin jami’an tsaro kafin gudanar da taron.
Haka kuma, kungiyar ta jaddada cewa ba za a gudanar da wani taron siyasa a wuraren taro ba, ko da kuwa an shirya gudanar da shi washegari, matuƙar ba a samu izinin jami’an tsaro ba.
Sanarwar ta fito ne daga shugabancin Kungiyar Masu Shirya Bukukuwa da Masu Wuraren Taro ta Jihar Kano.
