Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya miƙa saƙon ta’aziyya ga gwamnan Sokoto Dr Ahmad Aliyu, da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, da al’ummar jihar bisa rasuwar tsohon Ministan kuɗi na Najeriya kuma Sardaunan Sakkwato, Alhaji Abubakar Alhaji.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, inda sanarwar ta ce marigayin ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya.
Gwamna Abba ya bayyana marigayin a matsayin ƙwararren ma’aikacin gwamnati, masanin tattalin arziki kuma gogaggen jami’in diflomasiyya wanda ya ba da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da inganta harkokin mulki da hulɗar Najeriya da ƙasashen waje.
Gwamnan ya ce Alhaji Abubakar Alhaji ya sadaukar da rayuwarsa wajen bautawa ƙasa da kuma ci gaban Jihar Sokoto to, lamarin da ya sa ya samu karramawa da girmamawa saboda riƙon amana da hikimarsa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na cewa rasuwar tsohon ministan babban rashi ne ga jihar Sokoto da Najeriya baki ɗaya, tare da baiwa iyalansa da al’ummar Sokoto da ɗaukacin Najeriya juriyar babban rashin.
