Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da kashe Naira biliyan 45 wajen kafa tsarin tsaron lafiya da sa ido kan cututtuka a manyan filayen jiragen sama guda biyar na ƙasar nan.
Da ya ke bayyana haka bayan taron majalisar da shugaba Tinubu ya jagoranta jiya Laraba, ministan lafiya Farfesa Ali Pate ya ce an amince da fitar da kudin domin ƙarfafa hanyoyin gano cutar Ebola da sauran cututtuka masu haɗari kafin su shiga kasar nan.
Ya ce annobar COVID-19 ta bayyana raunin da ke cikin tsarin Najeriya na ganowa da kuma shawo kan cututtukan da za su iya shigowa ƙasar nan ta kan iyakoki.
Ya ƙara da cewa darussan da aka koya daga matakin da Najeriya ta dauka kan Ebola sun taimaka wajen tsara wannan sabon shiri.
Za a gudanar da aikin ne ƙarƙashin yarjejeniyar haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu na tsawon shekaru 20, inda kamfanin BioHealth Consortium zai tsara, samar da kuɗaɗe, ginawa, gudanarwa da kuma kula da cibiyoyin.
Filayen jiragen saman da za su amfana da shirin su ne, na Malam Aminu Kano da ke nan Kano da Murtala Muhammed da ke Legas da Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da filin Jirgin saman Fatakwal da na Akanu Ibiam da ke Enugu.
Ministan lafiyar ya bayyana cewa sama da fasinjoji miliyan 18 ne ke wucewa ta filayen jiragen saman kasar nan a kowace shekara, lamarin da ya sa inganta sa ido kan cututtuka a wuraren shigowa yake da matuƙar muhimmanci.
