Dagacin garin Dogon Kawo, da ke karamar hukumar Doguwa, Alhaji Kailani Yusuf, ya zargi Dan Amar din Kano kuma hakimin Doguwa, Alhaji Aliyu Harazumi da kokarin amfani da jami’an tsaro domin cin zarafinsa.
Dagacin ya ce hakimin ya sa jami’an tsaro su kama shi ba tare da sanin laifin da ya aikata ba duk kuwa da lauyansa da ya tura ga yansanda da kai korafi wurinsu domin dalili.
Idan za a iya tinawa dai, a cikin watan Oktoban da ya gabata wasu kafafen yada labarai sun rawaito cewa hakimin ya dakatar da dagacin garin na Dogon Kawo, Alhaji Kailani Yusuf kan zargin sa da yiwa Fulani karfa-karfar kwace gonakinsu tare da sayarwa.
Sai dai dagacin ya musanta duka tuhume-tuhumen tare da kalubalantar matakin ta hanyar shigar da korafinsa zuwa ga masarautar Kano.
Dagacin ya kuma ce hakimin, Alhaji Aliyu Harazumi ba shi da hurumin da dakatar da shi daga mukamin nasa.
Da muka tuntubi hakimin, ya tabbatar wa da Premier radio cewa, shi bai cire dagacin ba wakilin dagacin ya cire saboda zage-zagen sayar da wadancan gonaki.
Sai dai dagacin garin na Dogon Kawo, Alhaji Kailani Yusuf, ya zargi shi hakimin da kokarin amfani da jami’an tsaro wajen cin zarafinsa tare da tsoratar da shi.
Ya ce babu wata sanarwa kan dalilin da ya sa shi hada shi da jami’an tsaron kuma babu wata sanarwa kan laifin da aikata masa, saboda yake ganin masarautar Kano ya kamata su je kasancewarsu masu rike sarauta.
Kan wannan korafi mun tuntubi hakimin na Doguwa, Alhaji Aliyu Harazumi, wanda ya ce ya kai kara ga yansanda ne saboda kokarin bata masa suna da dagacin ke yi.