Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiJami'a zata fara Degree a bangaren tsafi da tsubbu.

Jami’a zata fara Degree a bangaren tsafi da tsubbu.

Date:

Jami’ar Exeter dake Birtaniya zata fara karatun Degree a bangaren tsafi da tsubbace tsubbace daga shekarar 2024.

Guda cikin jami’an makarantar da zai jagoranci darasin Farfesa Emily Selove ya ce za a fara karatun Degree na biyu a bangaren tsafi biyo bayan yawaitar masu nuna sha’awa a bangaren.

Jami’ar zata bada damar karantar tarihi da kuma tasirin tsafi a cikin al’umma a duniya.

Za a fara karatun ne a watan Satumba na shekarar 2024.

Kwararru a bangaren tarihi da adabi da ilimin falsafa da addini da sauran bangarori zasu nuna rawar da tsafi yake takawa a yammaci da gabashin duniya.

Za a bayar da darasin ne a kwalejin arabiya da nazarin addinin musulunci dake jami’ar.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...