Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMa'aikatar Mata Ta Jihar Kano Ta Musanta Zargin Sayarwa Da Kuma Lalalata...

Ma’aikatar Mata Ta Jihar Kano Ta Musanta Zargin Sayarwa Da Kuma Lalalata Da Yara A Gidan Marayu Na Kano.

Date:

Ma’aikatar harkokin mata ta jihar Kano ta barranta kanta daga wasu zarge-zargen da wasu mata suke yadawa, cewar gidan marayu na jihar Kano dake unguwar Nassarawa yana siyar da yara da kuma lalata da wasu daga cikinsu.

 

Kwamishiniyar harkokin mata ta jihar Kano, Dr. Zahra’u Muhammad Umar ce ta musanta zargin, lokacin da take zantawa da namema labarai a offishinta, kan wasu mata dake kokarin bata sunan ma’aikatar.

 

Tace matan da ke kokarin yin hakan, ma’aikatar mata ta jihar Kano ce, ta dauki nauyin su suka yi karatun likitanci, wanda bayan daya daga ciki mai suna Fatima Mohammed sani, wadda aka fi sani da Ladidi ta kammala karatun, gwamnatin Kano ta samar mata aiki a ma’aikatar lafiya ta jihar Kano.

 

A jawabinsa shugaban kwamatin kula da marayun Malam Kabiru Zubairu yace gidan marayun ko kwamishiniyar mata basu da ikon bayar da maraya ko daya har sai an bi dokokin da gwamnatin Kano ta sanya, ta hanyar yarjejeniya da kotu da jami’an tsaro kafin daukar maraya.

 

Kwaminishiyar matan ta tabbatar da cewa, zata cigaba da yin bakin kokarin ta wajan ganin an cigaba da kulawa da marayun da suke zaune a gidan marayun.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...