Fadar White House ta ƙaddamar da Trump TV mai watsa shirye-shirye sa’o’i 24
Fadar White House a Amurka ta ƙaddamar da wata sabuwar tashar watsa shirye-shiryen intanet mai suna “TRUMP TV: The Essentials Station”, wadda ke gabatar da jawabai, sanarwa da sauran shirye-shiryen da suka shafi Shugaban Amurka Donald Trump da gwamnatinsa.
An fara watsa shirye-shiryen tashar ne ranar Litinin, kuma ana iya kallonta ta shafin White House da kuma tashar YouTube. Fadar White House ta ce za a rika sabunta tashar cikin sauri da manyan jawabai, bidiyoyi da muhimman abubuwan da gwamnatin Trump ta gudanar.
“Trump TV tana watsa shirye-shirye yanzu, sa’o’i 24 a rana, kwana bakwai a mako, tare da sabunta abubuwan da ake watsawa a kai a kai,” in ji Fadar White House.
Ta ƙara da cewa, “Ba kowane muhimmin abu ne ya samu damar shiga talabijin ba, amma yanzu zai samu.”
Ƙaddamar da tashar na zuwa ne a lokacin da ake samun takaddama tsakanin gwamnatin Trump da wasu manyan kafafen yaɗa labarai na Amurka kan damar ‘yan jarida shiga Fadar White House.
CNN, MS NOW da Politico sun shigar da ƙara a kotun tarayya, suna kalubalantar matakin gwamnatin na hana ‘yan jaridunsu shiga Fadar White House. Rikicin ya kuma kawo cikas ga tsarin haɗin gwiwar kafafen talabijin wajen watsa hotunan abubuwan da shugaban Amurka ke gudanarwa.
Trump ya kare matakin gwamnatin tasa, yana zargin wasu kafafen yaɗa labarai da rashin yin adalci wajen rahotanninsu.
“Na yi imanin cewa waɗannan kafafen yaɗa labarai suna da alhakin yin adalci,” in ji Trump. “Idan kuma labaran ƙarya suke yaɗawa, ina ganin ina da alhakin hana su shiga.”
A farkon yada shirye-shiryen Trump TV, an nuna wasu tsofaffin bidiyoyi, ciki har da jawabin Trump a dutsen Mount Rushmore da kuma hotunan rantsar da shi a matsayin shugaban Amurka na 47 a shekarar 2025.
