
Aminu Abdullahi Ibrahim
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta yi amfani da tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026 wajen hana ƴan takarar da aka tabbatar suna da hannu wajen haddasa tashin hankali shiga zaɓe.
Akpabio ya bayyana hakan ne yayin zaman majalisar dattawa ranar Talata, bayan Sanata mai wakiltar Jigawa ta Arewa maso Yamma, Babangida Hussaini, ya yi zargin cewa an ga wani ɗan takarar jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, a jihar yana ɗauke da bindiga a wajen gangamin neman zaɓe.
Shugaban majalisar dattawan ya ce INEC na da ikon hana ɗan takara shiga zaɓe idan ta samu hujjojin farko masu ƙarfi da ke nuna cewa shi ko wakilansa sun haddasa ko suka tunzura mutane zuwa tashin hankali.
Ya kuma ce ya kamata a gudanar da bincike kan hoton da ake zargin ya nuna ɗan takarar yana riƙe da bindiga, domin tabbatar da sahihancinsa, musamman don kawar da yiwuwar an ƙirƙire shi da fasahar AI.
Akpabio ya jaddada cewa tanade-tanaden dokar zaɓen na 2026 na buƙatar cikakken aiki, ba tare da nuna bambanci tsakanin jam’iyyun siyasa ba.
Wannan na zuwa ne a yayin da Majalisar Dattawa ke nuna damuwa kan ƙaruwar rikicin siyasa da hare-hare kan wasu manyan ƴan siyasa gabanin zaɓen shekarar 2027.
Majalisar ta kuma buƙaci jami’an tsaro su gudanar da bincike kan hare-haren da aka ruwaito a kan Shugaba Bola Tinubu, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da Peter Obi, tare da gano waɗanda suka aikata su da kuma waɗanda ake zargin sun ɗauki nauyin rikice-rikicen.
