Duk da umarnin da kotu ta bayar ga hukumar tsaro ta DSS na a gaggauta mika matashiyar nan Walida yar asalin garin Hadeja a jihar Jigawa ga iyayen ta, har yanzu hukumar ba ta yi biyayya ga umarnin ba.
Shekaru 2 kenan tun bayan da aka zargi wani jami’in hukumar ta DSS Ifeanyi Festus da sace matashiyar.
Wakilan Premier Radio Abubakar Haruna Galadanci da Mustapha Kankarofi, sun je gidan su matashiyar da ke garin Hadeja a jihar Jigawa, inda suka gana da mahaifinta Malam Abdulhadi.
A cewar sa bakin cikin sace yar tasu ne yayi ajalin mahaifiyarta, ‘Kowa hankalinsa a tashe yake ni burina a dauki ‘ya ta a bani, da muake je ma ba a barni naga yarinyar ba, to binciken me zasuyi, bayan kotu ta bada umarnin a bani yata, sun juya mata addini sun mayar da ita kirista’.
Lauyan sa Barrister Kabiru Adamu yace zasu cigaba da bibiyar shari’ar har zuwa magaryar tukewa, ‘tunda umarnin kotu cewa akayi a sadar da yarinya ga iyayenta, kuma mun rubuta musu, mun zauna dasu mu gaya musu, yarinya kawai muke so, amma suka ce baza su bayar da ita ba’.
Har yanzu dai mahaifin yarinyar Malam Abdulhadi na kokawa kan abinda yace yafi karfinsa, sai dai zuba ido kawai tun da dais hi ba mai karfi ba ne.
