Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayyana sakamakon zaɓen cike gurbi na Dan Majalisar tarayyar ta Dawakin Kudu da Warawa a matsayin wata alama da ke nuna irin nasarar da jam’iyyar APC ke sa ran samu a babban zaɓen shekarar 2027.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, gwamnan ya ce yawan fitowar jama’a domin kaɗa ƙuri’a tare da gudanar da zaɓen cikin lumana ya nuna cewa al’ummar yankin na ci gaba da goyon bayan jam’iyyar APC da manufofinta.
Gwamna Abba ya ce an gudanar da zaɓen cikin adalci, gaskiya da sahihanci, lamarin da ya nuna ra’ayin masu zaɓe ba tare da wata tangarda ba, tare da yabawa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, bisa nasarar gudanar da zaɓen, tare da jinjinawa jami’an tsaro kan tabbatar da zaman lafiya kafin, lokacin da kuma bayan zaɓen.
A cewarsa, yadda aka gudanar da zaɓen da sakamakonsa sun ƙara tabbatar da amincewar jama’a ga tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya, tare da taya ɗan takarar APC murnar samun nasara, da yin kira gare shi da ya mayar da hankali wajen wakiltar al’umma yadda ya kamata domin cika burinsu.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito
Gwamna Yusuf na sukar jam’iyyar NDC bisa kasa tsayar da ɗan takara a zaɓen, inda ya bayyana ta a matsayin wata jam’iyya mara cikakken tushe a tsakanin al’umma.
