Gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin aikewa da jami’an tsaro na musamman aƙalla 200 domin samun horo a Turkiya ƙarƙashin wata yarjejeniya da ɓangarorin biyu suka cimma, wadda za ta fara aiki cikin gaggawa.
Ministan tsaron kasar nan, Christopher Musa ne ya sanar da wannan mataki bayan tattaunawarsa da takwaransa na Turkiyya, Yasar Guler, a wani ɓangare na taron diflomasiyya karo na 5 da ya gudana ranar Asabar.
To sai dai ministan ya kuma bayyana cewa baya ga wannan horo na jami’ai 200, akwai sauran yarjeniyoyin taimakon juna tsakanin Najeriyar da Turkiya a ɓangaren tsaro inda ƙasashen biyu za su ci gaba da aiki tare.
