Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ce babu wani bambanci tsakanin ‘ya’yan da ya haifa a cikinsa da yaran dake zaune gidan marayu na Nasarawa da sauran yara marasa galihun dake fadin Kano.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin gabatar da walimar Sallah daya gudanar da marayun dake gidan rainon yara na Nasarawa domin sanya farin ciki a zukatansu.
A cewar gwamna Abba kyautatawa da inganta rayuwar yaran, nauyi ne daya rataya a wuyan kowa domin a cikin su za’a iya samun shugabanni, malamai da sauran manyan mutane, la’akari da ilimi da kyakkyawar tarbiyyar da suke samu a gidan marayun.
Gwamnan ya kuma yabawa gudummawar da mawadata da kamfanoni ke bayarwa wajen tallafawa rayuwar marayun, tare da yin kira ga sauran masu hannu da shuni da su shiga cikin aikin na alheri domin samun lada a duniya da lahira.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na godewa shugabannin gidan marayun bisa yadda suke riƙe amanar kula da yaran, tare da samar musu da Kyakkyawar kulawa.
