Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari wani sansanin jami’an Hukumar Tsaro ta Civil Defense a ƙauyen Tsamiya da ke ƙaramar hukumar Bagudo a Jihar Kebbi, inda suka ƙone sansanin tare da yin garkuwa da wani mazaunin yankin.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun mamaye yankin ne cikin dare, inda suka banka wa sansanin NSCDC wuta kafin su yi awon gaba da wani mutum zuwa wurin da ba a sani ba.
Harin ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba da tashin hankali.
Mazauna yankin sun ce maharan sun yi amfani da manyan makamai tare da harbe-harbe domin tsoratar da jama’a yayin aiwatar da harin.
Sun kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara kaimi wajen kare yankunan da ke fama da hare-haren ’yan bindiga.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jami’an tsaro ba su sanar da kama waɗanda suka kai harin ko kuma ceto mutumin da aka sace ba.
