Hukumar kula da lafiya Matakin farko ta Kano, haɗin gwiwa da shugabannin ƙananan hukumomi 44 na jihar, sun amince da wani tsarin aikin bai daya mai matakai shida domin ƙarfafa ayyukan kiwon lafiya a matakin farko, inganta gaskiya da riƙon amana, da kuma kyautata shugabanci a harkar lafiya.
An cimma matsayar ne a wani taron rabin shekara na kwanaki biyu da suka gudanar mai taken ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Hukumar da Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Najeriya.
Taron ya kuma baiwa mahalartan sa damar duba ci gaban da aka samu, gano gibin da ke akwai, tare da tsara hanyoyin da za su taimaka wajen inganta harkokin kiwon lafiya a matakin ƙasa.
Da yake jawabi a wajen taron, Kwamishinan Lafiya na Kano Dr Abubakar Labaran Yusuf, wanda babban sakataren ma’aikatar ta jihar Shi ma Babban Sakataren Ma’aikatar Pharmacist Aminu Bashir ya wakilta ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su ƙara himma wajen tsare-tsare, bin diddigi da aiwatar da shirye-shiryen lafiya yadda ya kamata.
Shi ma Shugaban Hukumar kula da lafiyar a matakin farko ta Kano Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, ya jaddada muhimmancin ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin hukumar da ƙananan hukumomi domin cimma manufofin kiwon lafiya.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa daga cikin matakan da aka amince da su akwai samar da takaitaccen rahoton alamomin kiwon lafiya ga dukkan ƙananan hukumomi 44, tattara bayanan ra’ayi daga shugabannin ƙananan hukumomin kan tsare-tsaren lafiyarsu na watanni shida, sake horas da kwamitocin bada shawara na cibiyoyin lafiya, da kuma wayar da kan shugabannin sashen tsare-tsare da kididdiga domin samar da kasafin kuɗi ga ƙarin shirye-shiryen lafiya.
