Rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai ta bayyana cewa dakarunta sun kashe mayaƙan ƙungiyar ISWAP 48 yayin wasu hare-haren da aka gudanar a jihohin Borno da Yobe.
Rundunar ta ce an gudanar da ayyukan ne a garin Bitta da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno, da kuma Buni Yadi a Jihar Yobe, a ranakun 29 da 30 ga Oktoba, 2026.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Hedikwatar Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar a ranar Juma’a.
A cewar sanarwar, dakarun sun daƙile wani yunƙurin kai hari a garin Bitta, ta hanyar haɗin gwiwar sojojin ƙasa da tallafin jiragen yaƙi.
Rundunar ta bayyana cewa martanin da sojojin suka mayar ya tarwatsa maharan tare da jawo musu asara mai yawa.
Ta ƙara da cewa an kashe mayaƙan ISWAP 48 yayin farmakin, tare da ƙwato makamai da alburusai masu yawa daga hannun maharan.
Rundunar ta ce ayyukan na daga cikin ƙoƙarin da take yi na daƙile hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da kuma tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
