Rahotanni na cewa dakarun ƙasar nan sun yi nasarar kashe gwamnan ‘yan ta’adda yaran ƙasurgumin ɗanbindigar nan Adamu Aleiro, a wata arangama da suka yi a ƙaramar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara.
Rahotanni sun ce an fara bata-kashin ne ranar Asabar da yamma lokacin da ɓarayin dajin suka kai wa ‘yan sa-kai hari a ƙauyen Kunchin Kalgo.
Wani mazaunin yankin ya tabbatarwa da premier radio cewa yayin arangamar an kashe sama da ‘yan ta’adda sama da 80.
Inda yace Daga cikin waɗanda rahotanni ke cewa an kashe akwai Kachalla Iliya Sarki, wanda aka ce ɗa ne ga ƙasurgumin shugaban ɓarayin daji Ado Aleiro, tare da wani babban ƙasurgumin ɓarawon daji mai suna Dogo Bete.
Ana dai kallon jihar Zamfara a matsayin matattarar masu garguwa da mutane a kasar nan, ya yin da sau da dama mahukunta ke sanar da ɗaukar matakai na musamman domin murƙushe ƴan bindigar amma hakan ya gagara.
