Hukumar Shari’a ta Kano ta ƙaddamar da sabuwar kalandar Musulunci ta shekarar 1448 bayan hijira, domin sauƙaƙawa al’umma sanin ranakun ibadu da sauran muhimman lokutan addini.
Kwamishina na biyu a Hukumar Sheikh Ali Ɗan Abba, ne ya jagoranci ƙaddamar da kalandar a wani taro da aka gudanar a ɗakin taro na Coronation da ke Fadar Gwamnatin
Kano.
Sheikh Ali Dan Abba ya ce sanin ranakun kalandar Musulunci na da muhimmiyar rawa wajen gudanar da ibadu, musamman azumi, Hajji, Zakka da sauran muhimman lokutan addini.
A nasa jawabin, Shugaban Ma’aikatan fadar Gwamnatin Kano, Dr Sulaiman WALI, wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ƙaddamar da kalandar zai taimaka wajen samar da ingantaccen bayani kan ranaku da watannin Musulunci, tare da rage ruɗanin da ka iya tasowa wajen tantance muhimman ranakun addini.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Wali na bayyana kalandar a matsayin muhimmin abun da zai taimakawa al’umma wajen tsara harkokinsu bisa ka’idar Musulunci.
