Wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne sun yi garkuwa da ɗaliban makarantar Islamiyya 14 tare da malaminsu a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja.
Jaridar punch ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne yayin da ɗaliban da malaminsu suke wata gona.
Har yanzu ba’a bayar da cikakken bayani kan waɗanda suka kai harin ko matakan da hukumomin tsaro suka ɗauka domin ceto waɗanda aka sace ba.
