Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya yi Allah-wadai da matakin Shugaban Amurka, Donald Trump, na sassauta wasu takunkuman da aka kakabawa Rasha, domin ba ta damar samar da man dizal ga Amurka da kasuwannin duniya.
Trump ya ce ya cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawar wayar tarho da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin.
Zelensky ya bayyana cewa sassauta takunkuman ba tare da samun wata yarjejeniya mai ƙarfi da za ta rage rikicin ba, alama ce ta rauni, yana mai gargadin cewa hakan na iya bai wa Rasha damar tsawaita yaƙin da take yi da ƙasarsa.
A nasu ɓangaren, ’yan jam’iyyar Democrat da ke cikin Kwamitin Harkokin Waje na Majalisar Dattawan Amurka sun soki matakin, inda suka bayyana shi a matsayin cin amanar Ukraine da ƙawayen Amurka na Turai, tare da jefa tsaron Amurka cikin haɗari.
Rahotanni sun nuna cewa farashin man dizal ya tashi sosai tun bayan da Amurka ta fara yaƙi da Iran a watan Fabrairu, lamarin da ke ƙara matsin lamba kan jam’iyyar Republican ta Trump yayin da zaɓen rabin wa’adin Majalisar Dokokin Amurka ke gabatowa.
