Ministan yaɗa labarai Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wata ganawa da manema labarai, inda ya ce shugaban ƙasar yana sane da matsin tattalin arzikin da jama’a ke fuskanta sakamakon tashin farashin makamashi a kasuwannin duniya.
Ministan ya bayyana cewa matakin NNPCL na rage ribar sayar da man fetur an ɗauke shi ne domin samar da sauƙi na ɗan lokaci ga masu saye, ba wai don dawo da tsarin tallafin man fetur da aka cire a watan mayun 2023 ba, ya ce kamfanin zai yi amfani da wani ɓangare na ribarsa wajen rage kuɗin da masu saye ke biya.
Ya kuma ce tashin farashin man fetur ba Najeriya kaɗai ya shafa ba, domin farashin makamashi a duniya yana fuskantar sauye-sauye sakamakon rikice-rikicen ƙasashen duniya, gwamnatin ta ce tana duba wasu matakai da suka haɗa da ƙarfafa samar da makamashi a cikin gida da kuma faɗaɗa amfani da iskar gas wajen sufuri.
Sai dai matakin ya jawo muhawara daga ’yan siyasa da ƙungiyoyin ƙwadago, waɗanda suka yi tambayoyi kan yadda rangwamen zai amfanar da jama’a, musamman waɗanda ba sa sayen man fetur a gidajen mai na NNPCL, rahotanni sun kuma nuna cewa rangwamen Naira 66 kan lita yana da alaƙa da amfani da manhajar NNPCL da biyan kuɗi ta hanyar manhajar zamani.
Ministan ya ce gwamnatin na son a tabbatar da cewa ci gaban da ake samu a wasu alamomin tattalin arziki ya fara bayyana a rayuwar jama’a ta hanyar samar da ayyukan yi, ƙara ƙarfin saye da kuma rage tsadar kayayyaki da hidimomi, sai dai har yanzu ’yan Najeriya na ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsadar rayuwa.
