Rahotanni sun nuna cewa wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da matafiya 28 daga garin Zak da ke yankin Bashar a ƙaramar hukumar Wase ta jihar Filato.
Wani mazaunin yankin da ya tabbatar wa jaridar Daily Trust faruwar lamarin, ya ce waɗanda aka sace sun haɗa da maza, mata da ƙananan yara, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa garin Sabon Layi ne domin halartar taron Maulidi a ranar Lahadin da ta gabata.
A cewarsa, “Da safiyar Litinin ne matafiya da ke bin hanyar suka hango wata mota a tsaye a kan titi, wadda daga bisani aka gano mallakin wani shugaban al’ummar garin Zak ce. Bayan dubawa ne aka fahimci cewa ita ce motar da ke ɗauke da matafiyan da aka sace.”
Wani mazaunin garin ya ce har zuwa yanzu babu wani sahihin bayani kan inda mutanen da aka sace suke, lamarin da ya jefa iyalansu da al’ummar yankin cikin fargaba.
Da yake martani kan lamarin, kakakin rundunar ’yan sandan jihar Filato, SP Alabo Alfred, ya ce rundunar ta samu rahoton faruwar lamarin kuma ta fara bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru.
