Saurari premier Radio
23.4 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiƊanyen man da ƙasar nan ke haƙowa ya ƙaru da kashi huɗu...

Ɗanyen man da ƙasar nan ke haƙowa ya ƙaru da kashi huɗu cikin ɗari.

Date:

Danyen man da kasar nan ke hakowa ya karu da kashi 4 cikin dari, zuwa ganga miliyan 1 da dubu 230 a watan maris din da ya gabata.

Kamar yadda kididdigar hukumar kula da hakar mai ta kasa ya nuna, said ai cigaban ya gaza abinda gwamnati ke fatan samu, na ganga miliyan 1 da dubu 780 domin ta samu damar gabatar da ayyukan dake cikin kasafin kudi na shekarar 2024.

Duka duka dai Najeriya ta hako ganga miliyan 1 da dubu 447 a watan na Maris, to sai dai an samu ci baya idan aka kwatanta da watannin Janairu da fabrairu inda aka hako ganga miliyan 1 da dubu 530 da kuma ganga miliyan 1 da dubu 643.

Karamin ministan mai Senator Heineken Lokpobiri ya jaddada matsayar gwamnati na hako ganga m,iliyan 2 kafin karshn shekarar da muke ciki.

Ministan ya dora alhakin koma bayan da aka samu kan ayyukan tsagerun Neja Delta dake lalata bututu, da hakan ya hana KASAR NAN cimma burinta na samar da ganga miliyan 1 da dubu 500 a kullum kamar yadda kungiyar OPEC ta sahale mata.

Najeriya dai ta dade tana fuskantar kon gaba kon baya a fannin hakar mai a nahiyar Afrika saboda ayyukan yan tada kayar baya da tsagerun Neja Delta da kan fasa bututu, da kuma barayin danyen mai da kan fiytar dashi zuwa wasu sassa na duniya.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...