Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaƘarin albashin kashi 25 zuwa 35 na gwamnatin tarayya zai fara aiki...

Ƙarin albashin kashi 25 zuwa 35 na gwamnatin tarayya zai fara aiki ɗaya ga watan Janairun bana.

Date:

Gwamnatin tarayya ta yi wa ma’aikatanta karin albashi da kashi 25 zuwa 35 cikin dari, yayin da su kuma ’yan fansho suka samu karin kashi 20 zuwa 28 na abun da suke karba karshen kowanne wata.

Sanarwar da kakakin hukumar albashi ta kasa, Emmanuel Njoku ya fitar, ta ce karin zai fara aiki daga ranar daya ga watan Janairun bana.

Kungiyar kwadago dai ta dade tana neman a yi wa ma’aikata karin albashi, bisa la’akari da yadda farashin kayan masarufi ya yi tashin gwauron-zabo a ƙasar nan, tun bayan janye tallafin mai ranar 29 ga watan Mayun bara, lokacin da aka rantsar da shugaba Bola Ahmad Tinubu.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa, kungiyar ma’aikatan jami’a ta ce mambobinta ba za su amince da mafi ƙarancin albashin da ya fara da Naira dubu dari uku ba.

Latest stories

Related stories