
Aminu Abdullahi Ibrahim
Ƙungiyar Isa Wali ta horas da yara mata kimanin 200 domin ƙarfafa iliminsu da koyar da su sana’o’in dogaro da kai, a wani yunƙuri na samar musu da makoma mai kyau.
Shugabar ƙungiyar, Amina Hanga, ce ta bayyana haka yayin taron yaye yaran da aka gudanar a nan Kano.
Ta ce an zabo yaran ne daga unguwanni daban daban na jihar Kano kuma wannan ne karo na biyar da suke yaye daliban.
A nasa ɓangaren, daya dagacikin iyayen daliban da aka yaye Sani Ibrahim daga unguwar Kawo, ya bayyana farin cikinsa bisa damar da aka bai wa ‘yarsa ta shiga cikin darussan ƙungiyar.

Shi ma Mai Unguwar Daurawa, Yusuf Sulaiman, da ya halarci taron ya godewa kungiyar ta Isa Wali Empowerment tare da yin kira ga sauran kungiyoyi wajen yin koyi da ita.
