
Hukumar Kula Da Alhazan Najeriya (NAHCON) ta bayyana cewa maniyyata 2,717 ne ba su samu damar zuwa aikin Hajjin wannan shekara ba sakamakon biyan kudin kujera a ƙurarren lokaci.
Cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Yaɗa Labarai ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar, ta bayyana cewa, duk da gazawar hukumar wajen neman ƙarin wa’adin rajista daga hukumomin Saudiyya, an samu biza 13,217 daga cikin maniyyata 14,158 da kamfanonin yawon buɗe ido suka yi wa rijista.
Hukumar ta nemi afuwar mutanen da lamarin ya shafa, tana mai jaddada cewa zuwa Hajji kira ne na Ubangiji.
Haka kuma, hukumar ta yi kira ga maniyyata da su riƙa biyan kuɗinsu a kan lokaci, domin kauce wa irin wannan matsala a nan gaba.
Hukumomin Saudiyya sun ware wa Najeriya kujeru 95,000 domin aikin Hajjin bana, yayin da NAHCON ke ci gaba da kokarin sauƙaƙa tafiyar maniyyata da tabbatar da ingantacciyar gudanarwa.