Tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan, ya ce babban zaɓen 2027 zai zama wani muhimmin gwaji ga balagar dimokuraɗiyyar Najeriya, yana mai kira ga ’yan ƙasa da su fifita zaman lafiya, haɗin kai da adalci.
Jonathan ya bayyana hakan ne a cikin saƙonsa na bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai, inda ya ce Najeriya ta fuskanci ƙalubale daban-daban tun bayan samun ’yancin kai, amma juriyar al’ummarta ta taimaka wajen shawo kansu.
Tsohon shugaban ƙasar ya buƙaci ’yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa da fata da kuma kishin ƙasa, tare da yin aiki tare domin samun ci gaba mai ɗorewa, ya kuma jaddada muhimmancin shugabanni su kasance masu ɗaukar nauyi, kishin ƙasa da bin ƙa’idojin doka.
Jonathan ya ce yayin da ake tunkarar lokacin zaɓe, ya kamata ’yan Najeriya su guji duk wani abu da zai iya kawo tashin hankali ko raba kan al’umma, tare da ba da fifiko ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Ya kuma yi kira da a mai da hankali wajen magance matsalolin tattalin arziki da zamantakewa ta hanyar shugabanci nagari, riƙon amana da bin doka, yana mai cewa Najeriya na da damarmaki masu yawa idan aka yi amfani da albarkatun ƙasa yadda ya kamata.
A ƙarshe, Jonathan ya buƙaci ’yan Najeriya su ci gaba da taka rawar da ta dace wajen gina ƙasa mai zaman lafiya, tsaro da adalci, domin amfanin zamanin yanzu da masu zuwa.
