Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi kira ga mambobin Jam’iyyar APC da suka nuna rashin jin daɗi bayan zaɓen cikin gida da su ajiye saɓani a gefe, su haɗa kai domin jam’iyyar ta shiga zaɓen shekarar 2027 cikin haɗin kai da ƙarfi.
Gwamnan ya ce koke-koke da rashin jituwar da suka biyo bayan zaɓen fidda gwani ba sabon abu ba ne a tsarin dimokuraɗiyya, yana mai jaddada cewa sasanci da haɗin kai su ne ginshiƙan nasarar kowace jam’iyya.
Inuwa Yahaya ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da kwamitin sasanta rikice-rikicen APC a Jihar Gombe, wanda aka kafa domin sauraron koke-koken da suka biyo bayan tarukan jam’iyyar da zaɓen cikin gida.
Ya ce kafa kwamitin na daga cikin dabarun da jam’iyyar ta ɗauka domin dawo da haɗin kai tsakanin mambobinta da kuma tabbatar da APC ta shiga zaɓen 2027 a matsayin jam’iyya mai ƙarfi da haɗin kai.
Gwamnan ya kuma umarci mambobin kwamitin da su gudanar da aikinsu cikin adalci, gaskiya da rashin son kai, tare da kiyaye sirrin bayanan da masu ƙorafi za su gabatar domin samar da mafita mai ɗorewa ga rikicin cikin gida na jam’iyyar.
