Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiZaben Tinubu ne mafita ga tallalin arzikin kasar nan-kungiyar 'Drone Marshalls'

Zaben Tinubu ne mafita ga tallalin arzikin kasar nan-kungiyar ‘Drone Marshalls’

Date:

Kungiyar yakin neman zaben Bola Ahmad Tinubu Mai suna ‘Drone Marshalls’ ta ce babu abinda zai iya gyara tattalin arzikin kasar nan face zaben Tinubu a matsayin shugaban kasa.

 

Jami’in hulda da jama’a na kungiyar Ibrahim Sulaiman Ahmad ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai ranar Lahadi a nan Kano.

 

Ya ce idan aka yi la’akari da rawar da ya taka wajen habaka tattalin jihar Lagos lokacin da yake gwamna lallai ya cancanci a bashi kasar nan ya gyara.

A cewarsa Tinubu ya habaka tattalin arzikin jihar Lagos daga kaso 20 zuwa kaso 85 cikin dari.

 

Haka Kuma a tsahon shekarun da ya dauka yana gwamnan ya taba rayuwar mutane da dama inda ya maishesu mutane.

 

Ibrahim ya ce ko a baya sai da gwamnatin PDP a wancan lokacin ta dakatar da biyan kudin kananan hukumomi amma sai da Tinubu ya samo hanyar da ya ci gaba da kula da su.

 

A don hakan ne wanna kungiya ta ce ba ta ga wanda ya fi cancanta ya zama shugaban kasa ba fiye da Bola Ahmad Tinubu.

 

Kungiyar ta kuma bukaci al’ummar jihar Kano da su fito kwansu da kwarkwata domin kada masa kuri’a lokacin zabe.

Latest stories

Related stories