Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt dubu goma tare da isar da ita ga masu amfani, idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Obi ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, yayin wani taron tattaunawa da jama’a a birnin Onitsha na jihar Anambra, inda ya ce shi da abokin takararsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, sun yi nazari kan matsalolin da ke addabar ɓangaren wutar lantarki a Najeriya.
A cewarsa, Najeriya na samarwa da kuma rarraba kusan megawatt dubu huɗu ne a halin yanzu, amma sun shirya ɗaga adadin zuwa aƙalla megawatt dubu goma a lokacin mulkinsu.
Obi ya kuma ce ba za su riƙa ɗora alhakin matsalolin ɓangaren wutar lantarki kan wasu ba, domin sun fahimci ƙalubalen da ke akwai kuma suna tsara hanyoyin magance su.
Sai dai alkaluman Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya, NERC, sun nuna cewa matsakaicin wutar da aka samar a kowace awa a zangon watanni uku na biyu na shekarar 2026 ya kai megawatt 4,022.40.
A nata ɓangaren, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa ƙarfin da Najeriya ke da shi na samar da wutar lantarki ya ƙaru daga megawatt dubu goma sha uku zuwa dubu goma sha huɗu, duk da ƙalubalen da ake fuskanta wajen samarwa da rarraba wutar.
Batun wutar lantarki na cikin muhimman batutuwan da ake tattaunawa a siyasar Najeriya, yayin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na ranar 16 ga Janairun 2027.
